Ibrahimovic zai buga karawa da Barca

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ce za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai

Zlatan Ibrahimovic zai buga wasan da Barcelona za ta karbi bakuncin Paris St-Germain a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata

Ibrahimovic bai buga wasan farko da Barca ta doke PSG 3-1 a faransa ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi daga buga wasan.

Dan kwallon Barcelona Andres Iniesta zai murmure kafin karawar duk da fitar da shi da aka yi daga filin wasa a kan gadon daukar marasa lafiya ranar Asabar.

Kyaftin din PSG ba zai buga wasan ba, sakamakon jinya da yake yi, a wasan farko ma sai David Luiz ne ya chanje shi.

PSG tana bukatar cin kwallaye uku a ragar Barcelona ba tare da an zura mata kwallo ba idan har tana fatan kai wasan daf da na karshe a gasar.