Barcelona ta doke Paris St-Germain da ci 2-0

Neymar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon da Barcelona ta dauki kofin zakarun Turai tun a shekarar 2011

Barcelona ta doke Paris St-Germain da ci 2-0 ta kuma kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a ranar Talata.

Barcelona ta zura kwallaye biyu ne a raga ta hannun Neymar a minti na 14 da fara tamaula, sannan ya kara ta biyu saura minti 11 a tafi hutun rabin lokaci.

A karawar farko da suka yi a Faransa a makon jiya, Barcelona ce ta samu nasara a fafatawar da ci 3-1.

A jumullar karawar da suka yi Barcelona ta doke PSG kenan da kwallaye 5-1, kuma rabon da Barca ta dauki kofin zakarun Turan tun a shekarar 2011.