Liverpool za ta katange filin atisayenta

Liverpool Training Ground
Image caption Za a dunga katange filin ne idan Liverpool za ta yi atisaye

Hukumar gudanarwar birnin Liverpool ta amince da bukatar da kungiyar Liverpool ta gabatar mata na shirin katange filin da 'yan wasanta suke yin atisaye.

Kungiyar na fatan kawo karshen yadda 'yan kallo suke kallon yadda kungiyar ke yin atisaye da kuma daukar hoton bidiyo a filin da ke Reds' Melwood Drive complex.

Hukumar gudanarwar ta goyi da bayan Liverpool ta katange filin da bangon zai kai tsawon mita biyar wanda zai taimaka wajen hana 'yan kallo daukar hotuna.

Kulob din ya ce hakan zai kawo karshen kutse da ake yi cikin filin, kuma zai sa ciyayin wurin su girma suna kuma samun kulawar da ta kamata.

Kuma Liverpool din ta ce kusan shekara guda da ta wuce ne ta mika bukarar katange filin atisayen ga hukumar birnin.