Falcao yana son ya ci gaba da zama a United

Radamel Falcao Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwallaye hudu Falcao ya ci wa United a wasanni 25 da ya buga

Dan kwallon Monaco Radamel Falcao ya ce yana son ya ci gaba da taka leda a badi a kulob din Manchester United.

Monaco ta ce da United kadai take tattauna wa don ganin dan kwallon da yake wasa aro a Old Trafford zai koma can kacokan.

Falcao ya koma United buga tamaula aro ne a watan Satumbar 2014, kuma ya zura kwallaye hudu daga wasannin 25 da ya buga a bana.

Shugaban Monaco Vadim Vasilyev ya ce suna jiran United ya yanke hukuncin idan zai dauki dan kwallon a shekara mai zuwa.

A kwantiragin da United da Monaco suka kulla a baya, United za ta biya kudin Falcao sama da fam miliyan 43 domin ya ci gaba da murza leda a Old Trafford a badi idan tana bukatar hakan.