Smalling zai ci gaba da murza leda a United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Smalling ya shafe shekaru biyar a Old Trafford

Dan kwallon Manchester United Chris Smalling ya tsawaita kwantaraginsa har zuwa watan Yunin 2019 domin ci gaba da taka leda a United.

Dan shekaru 25, ya koma United ne daga Fulham a shekara ta 2010 inda ya lashe kofunan Premier biyu a Old Trafford.

Kocin United, Louis van Gaal ya ce "Chris na daga cikin 'yan wasan da muke ji da su a kulob dinmu."

Smalling ya wakilci Ingila a matakin 'yan kasa da shekaru 18 da 20 da kuma 21.

Sannan ya soma buga babbar tawagar kwallon kasa a watan Satumbar 2011 a wasa tsakaninsu da Bulgaria.