Wasannin Premier Nigeria gasar mako na biyar

Nigerian Premier week 5 Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na biyar a filaye daban-daban a Nigeria

Nasarawa United za ta karbi bakuncin mai rike da kofin Premier Nigeria Kano Pillars a cigaba da gasar wasannin mako na biyar.

A garin Fatakwal wasanni biyu za a fafata a inda Sharks za ta kara da Bayelsa United, sai kuma Dolphins da Enugu Rangers.

Sauran wasannin da za a kara Kwara United za ta ziyarci Shooting Stars sai kuma kai ruwa rana tsakanin Heartland da Abia Warriors.

Ga jerin wasannin da za a buga

  • Taraba FC - Enyimba Aba
  • Sharks FC - Bayelsa United
  • Ifeanyi Uba - Lobi Stars
  • Giwa FC - Akwa United
  • Dolphins FC - Enugu Rangers
  • El-Kanemi Warriors - Sunshine Stars
  • Wikki Tourists - Warri Wolves
  • Heartland FC - Abia Warriors FC
  • Shooting Stars FC - Kwara United
  • Nasarawa United FC - Kano Pillars