Madrid ta kai wasan daf da karshe a kofin Turai

Javier Hernandez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ta dauki kofin zakarun Turai sau 10

Real Madrid ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin zakarun Turai, bayan da ta doke Atletico da ci daya mai ban haushi a ranar Laraba.

Madrid ta ci kwallonta daya ne tilo ta hannun Javier Hernández saura minti biyu a tashi daga karawar.

Atletico ta karasa fafatawar ne da 'yan wasa 10 a cikin fili bayan da aka bai wa Turan jan kati.

A wasan farko da suka yi a gidan Atletico a makon jiya tashi suka yi babu ci.

Da wannan nasarar Real Madrid wacce take rike da kofin bara kuma karo na 10 ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin bana.