Da kyar Sevilla ta kai wasan daf da karshe a Europa

Sevilla FC Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar Juma a ne uefa za ta raba jaddawalin wasannin daf da karshen

Mai rike da kofin zakarun Turai na Europa Sevilla ta kai wasan daf da karshe a gasar da kyar, bayan da suka tashi 2-2 da Zenith St Petersburg a Rasha ranar Alhamis.

Sevilla ce ta doke Zenith da ci 2-1 a Spaniya, a inda jumullar haduwa Sevilla ta kai bantenta da ci 4-3.

Kungiyar Fiorentina da kuma Napoli suma sun kai wasan daf da karshe a gasar da kuma kulob din Dnipro na Ukraine.

Tun a baya hukumar kwallon kafar Turai wato UEFA ta ce ba za ta hada wasa ba tsakanin wata kungiya daga Rasha da kuma ta Ukraine, domin kauce wa rikicin da ake yi a kudancin Ukraine din.