West Brom da Liverpool sun tashi 0-0

Westbrom Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gerrard ya buga wa Liverpool wasa na 500 a Premier

West Brom da Liverpool sun tashi wasa canjaras a gasar Premier wasan mako na 34 da suka buga ranar Asabar.

Sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne dukkan kungiyoyin suka dunga kai wa juna hare-hare, amma haka suka tashi wasan babu ci.

Kyaftin din Liverpool ya shiga jerin tarihin 'yan wasan da suka buga wa kungiya daya wasanni 500, da suka hada da Ryan Giggs 632 da Jammie Carriger 508.

Da wannan sakamakon Liverpool ta ci gaba da zama a matakinta na biyar a teburin Premier da maki 58, West Brom kuwa tana matsayi na 13 da maki 38.

Sauran wasannin da aka buga Leicester ta doke Burnley da ci 1-0, kuma hakan ya sa ta fice daga rukunin kungiyoyi uku da za su iya barin Premier a bana.

Newcastle kuwa rashin nasara ta yi da ci 3-2 a hannun Swansea har gida, yayin da wasa tsakanin Southampton da Tottenham suka tashi 2-2.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Southampton 2 - 2 Tottenham
  • Burnley 0 - 1 Leicester
  • Crystal Palace 0 - 2 Hull City
  • Newcastle 2 - 3 Swansea City
  • QPR 0 - 0 West Ham Und
  • Stoke 1 - 1 Sunderland
  • West Brom 0 - 0 Liverpool