Arsenal da Chelsea sun tashi wasa duro

Arsenal Chelsea
Image caption Arsenal ta koma mataki na uku a kan teburin Premier da maki 67

Kungiyar Arsenal da Chelsea sun tashi wasa babu ci a gasar Premier wasan mako na 34 da suka fafata a Emirates.

Wannan shi ne karawa ta 13 da aka yi tsakanin Wenger da Mourinho, inda Mourinho ya lashe wasanni bakwai suka buga canjaras a karawa shida da suka yi.

Chelsea tana matakinta na daya a teburin Premier da maki 77, yayin da Arsenal ta fada mataki na uku a teburin da maki 67.

Ranar Talata ne Chelsea za ta buga kwantan wasanta da Leicester City, kuma idan ta cinye wasan za ta dauki kofin Premier bana kuma na biyar jumulla.

Arsenal wacce za ta buga wasan karshe da Aston Villa ranar 30 ga watan Mayu, za ta kara ne da Hull City a gasar Premier.