Everton ta doke Man United da ci 3-0

Everton vs United
Image caption Everton za ta kara da Aston Villa a Villa Park a wasan mako na 35

Everton ta hada maki uku a gasar Premier wasan mako na 34, bayan da ta doke Manchester United da ci 3-0 a Goodison Park.

Everton ta zura kwallon farko ne ta hannun McCarthy a minti na biyar da fara tamaula, sannan kuma Stones ya kara ta biyu saura minti 10 a je hutun rabin lokaci.

Mirallas ne ya kara ta uku a ragar United, kuma da wannan nasarar da Everton ta samu yasa ta matsa sama zuwa mataki na 10 a teburin Premier da maki 44.

United kuwa ta koma matsayi na hudu a teburin Premier da maki 65, bayan da Manchester City ta doke Aston Villa da ci 3-2 a Ettihad ranar Asabar.

Everton za ta ziyarci Aston Villa a wasan mako na 35 a Villa Park, yayin da Manchester United za ta karbi bakuncin West Brom a Old Trafford.