Kano Pillars ta doke Taraba FC da ci 2-1

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Pillars ta hada maki tara daga wasanni hudu da ta yi

Kano Pillars ta samu nasara a kan Taraba FC da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na shida da suka yi a Kano ranar Lahadi.

Pillars ce ta fara zura kwallo ta hannun Azeez Shobowale, a inda Taraba FC ta farke kwallo ta hannun Usman Mohammed a bugun fenariti kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Moses Ekpai ya ci wa Pillars kwallo ta biyu a minti na 51, wanda hakan yasa ta hada maki tara a wasanni hudu da ta yi kenan.

sauran sakamakon wasannin da aka buga Enyimba ta doke Sharks da ci 3-2 a wasan hamayya, yayin da Enugu Rangers ta zura kwallaye 3 da nema a ragar El-Kanemi.

Karawa tsakanin Lobi da Giwa FC da kuma wasan Bayelsa United da Gabros tashi suka yi canjaras.

Hukumar gudanar da gasar ta Premier ta dage karawa tsakanin Warri Wolves da Heartland zuwa ranar Litinin da safe, sakamakon ruwan sama da ya hana a buga wasan.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi:

  • Enyimba 3-2 Sharks
  • Bayelsa Utd 0-0 Gabros FC
  • Lobi Stars 1-1 Giwa FC
  • Akwa Utd 2-0 Dolphins
  • Rangers 3-0 El-Kanemi
  • Sunshine Stars 3-2 Wikki
  • Abia Warriors 1-0 Shooting Stars
  • Kwara Utd 1-0 Nasarawa Utd