Kano Pillars za ta kara da Taraba FC

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Giwa FC ce ke mataki na daya a teburin Premier da maki 10

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za ta karbi bakuncin Taraba FC a ci gaba da gasar Premier wasannin mako na shida ranar Lahadi.

Kano Pillars wacce ta yi rashin nasara a hannun Nasarawa United da ci 2-1 a makon jiya, tana mataki na 11 a tebrurin Premier da maki 6 daga wasanni uku da ta yi.

A makon jiya ne Taraba FC ta yi rashin nasara a hannun Enyimba har gida da ci daya mai ban Haushi, kuma tana da maki bakwai a mataki na 8 a kan teburn Premier.

Sauran wasannin da za a buga Warri Wolves za ta karbi bakuncin Heartland, yayin da Giwa FC wadda take matsayi na daya a teburin Premier za ta ziyarci Lobi Stars.

A garin Enugu kuwa za a kara ne tsakanin Enugu Rangers da El Kanemi Warriors, sai kuma wasan hamayya tsakanin Enyimba da Sharks a garin Aba.

Ga wasannin da za a buga ranar Asabar:

  • Enyimba vs Sharks
  • Bayelsa Utd vs Gabros FC
  • Lobi Stars vs Giwa FC
  • Akwa Utd vs Dolphins
  • Rangers vs El-Kanemi
  • Sunshine Stars vs Wikki
  • Warri Wolves vs Heartland
  • Abia Warriors vs Shooting Stars
  • Kwara Utd vs Nasarawa Utd
  • Kano Pillars vs FC Taraba