Robben zai koma buga tamaula ranar Talata

Arjen Robben Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Likitocin Munich ne za su tabbatar da idan Robben zai iya wasa ranar Talata

Dan kwallon Bayern Munich Arjen Robben zai koma murza leda bayan da ya yi jinyar makwanni shida.

Robben zai koma taka leda a gasar cin kofin kalubalen Jamus wanda Munich za ta kara da Borussia Dortmund a wasan daf da karshe.

Munich -- wacce take harin lashe kofuna uku a bana -- ta dauki kofin Bundesliga a karshen makon jiya, sau 25 ke nan.

Kocin Dortmund, Jurgen Klopp -- wanda zai bar kungiyar a bana -- yana fatan lashe kofi na hudu a shekaru bakwai da ya yi a kungiyar, bayan da ya lashe Bundesliga biyu da kuma na Kalubale daya.

Daya wasan daf da karshen da za a buga shi ne tsakanin Arminia Bielefeld da kuma Wolfsburg a ranar Laraba.