Munich ta lashe kofin Bundesliga karo na 25

Bayern Munich Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Munich ta dauki kofin Bundesliga karo na 25 kenan

Bayern Munich ta dauki kofin Bundesliga na bana kuma na uku a jere, bayan da ta doke Hertha Berlin da ci daya mai ban haushi ranar Lahadi.

An fara gasar cin kofin Bundesliga a shekara ta 1963, kuma Munich ta dauki kofin bana duk da saura wasanni shida a kammala gasar bana, kuma na 25 jumulla.

Munich din kuma ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin zakarun Turai da kuma kofin kalubalen Jamus a bana,

Bayern tana fatan lashe kofuna Jamus guda biyu a shekaru biyu a jere, da kuma daukar kofuna uku a cikin shekaru uku.

Koci Guardiola ya lashe kofunan gasar cikin gida guda biyar a shekaru shida da ya yi yana horar da tamaula, hudu daga ciki da kulob din Barcelona, guda biyu da Bayern.

Bayern za ta fafata da Borussia Dortmund a wasan daf da karshe a kofin kalubalen Jamus ranar Talata, sannan ta kara da Barcelona a wasan daf da karshe a kofin zakarun Turai a watan Mayu,