Hazard ya zama gwarzon gasar Premier

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mourinho ya ce darajar Hazard ta kai fan miliyan 200

Eden Hazard ya lashe kyautar dan kwallon kafar gasar Premier da ya fi yin fice a bana bayan ya taimaki Chelsea ta haskaka.

Hazard wanda yake taka leda a Chelsea ya ci kwallaye 13 a gasar Premier, sannan ya taimaka aka ci kwallaye takwas a wasannin Premier 33 da ya buga a bana.

Hazard mai shekaru 24 ya ce "Na yi matukar murna kuma ina saran wata rana ni ne zan zaman wanda ya fi kowa a duniya."

Dan kwallon Tottenham Harry Kane ne ya lashe kyautar matashin dan wasan da ya fi haskakawa a gasar.

Haka kuma 'yar wasan Chelsea, Leah Williamson ce ta lashe kyautar matashiyar 'yar wasa da ta fi yin fice a gasar Premier ta Mata.

Tawagar premier a bana:

David De Gea (Manchester United); Branislav Ivanovic (Chelsea), John Terry (Chelsea), Gary Cahill (Chelsea), Ryan Bertrand (Southampton); Nemanja Matic (Chelsea); Alexis Sanchez (Arsenal), Philippe Coutinho (Liverpool), Eden Hazard (Chelsea); Diego Costa (Chelsea), Harry Kane (Tottenham).