An sallami Oscar na Chelsea daga asibiti

Oscar Ospina Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oscar yana daga cikin kashin bayan Chelsea a gasar wasannin bana

Likitoci sun sallami dan kwallon Chelsea Oscar daga asibiti bayan da suka duba lafiyarsa, sakamakon raunin da ya ji a kansa a wasan Premier da suka yi da Arsenal.

Dan wasan ya yi karo da mai tsaron ragar Arsenal David Ospina a minti na 16, kuma a dalilin haka ne yasa aka canja shi a wasan bayan da aka tafi hutu.

Mourinho ya ce "Jami'an kulob din sun firgita tun a farko kan raunin da dan kwallon ya ji, amma ya murmure kuma a gida ya yi barci zai ma yi atisaye da sauran 'yan wasa".

Sabuwar dokar da hukumar gasar Premier ta kafa tace likitan kungiya ne zai yanke hukunci idan dan kwallo zai iya ci gaba da wasa a lokacin da ya gamu da buguwa a kansa.