"Muna alfahari da yadda ake gudanar da Arsenal"

Arsenal Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal za ta buga wasan karshe a kofin kalubale da Aston Villa a watan Mayu

Arsenal ba ta mayar da hankali kan sai ta lashe kofin zakarun Turai fiye da kowace gasa ba in ji shugaban kulob din Ivan Gazidis.

A karkashin koci Arsene Wenger, Gunners ta kai wasan karshe a kofin Turai a shekarar 2006, sai dai an cire ta a gasar bana a wasan zagaye na biyu kuma karo na biyar kenan a jere.

Shugaban ya ce ba wai daukar kofin zakarun Turai bane a gabansu, illa dai faranta wa magoya baya yadda ake gudanar da kulob din.

Gazidis, wanda ya koma Arsenal a shekarar 2009, ya fadi haka ne a wajen taron da kungiyar kawar da wariyar launin fata ta shirya.

A shekarar 2011 ne Arsenal ta zama daya daga cikin kungiyoyi biyu da suka cika ka'idojin kauce wa wariyar launin fata da bayar da damarmaki.