Hull City ta doke Liverpool da ci 1-0

Hull Liverpool
Image caption Liverpool tana mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 58

Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Hull City da ci daya mai ban haushi a kwantan wasan Premier da suka buga ranar Talata.

Hull City ta zura kwallo tilo ne a ragar Liverpool ta hannun Dawson saura minti takwas a tafi hutun rabin lokaci a KC Stadium.

Da wannan nasarar Hull ta matsa sama zuwa mataki na 15 a teburin Premier da maki 34, yayin da Liverpool tana nan dai a matsayinta na biyar a teburin da maki 58 iri daya da Tottenham.

Hull City za ta karbi bakuncin Arsenal a ranar Litinin, a inda Liverpool za ta buga wasanta na gaba da QPR ranar Asabar a Anfield.