PSG ba za ta sayar da manyan 'yan wasanta ba

PSG Players Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption PSG tana fatan lashe kofuna uku a bana

Shugaban kulob din Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi ya ce ba zai sayar da manyan 'yan wasansa ba a karshen kakar wasan bana.

Cikin manyan 'yan wasan da PSG ba zai rabu da su ba a banan sun hada da Zlatan Ibrahimovic da Edinson Cavani da kuma Javier Pastore.

Haka kuma shugaban ya ce ba zai sayar da koci Laurent Blanc wanda yake daf da lashe kofuna uku da kulob din a bana.

Kulob din Barcelona ne ya fitar da PSG daga gasar cin kofin zakarun Turai a wasannin daf da na kusa da karshe.

Tun a baya anyi ta rade-radin cewar kungiyoyin gasar Premier suna zawarcin Cabani da Pastore.