Za a sayar da West Bromwich Albion

west Brom Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Brom tana mataki na 13 a kan teburin Premier bana

Mutanen da suka mallaki kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion sun ce za su sayar da kulob din daga nan zuwa karshen watan gobe.

Shugaban kulob din ne Jeremy Peace ya sanar da hakan, yana mai cewa yana son sayar da West Brom din mai buga gasar Premier a kan fam miliyan 150.

Rukunan kamfanoni daga gabas ta tsakiya da Amurka sun bayyana sha'awar sayen kulob din, amma suna shirin yin tayin fam miliyan 40.

West Brom -- wanda yake shekara ta biyar a gasar Premier -- yana mataki na 13 a kan teburin Premier bana kuma ya ci ribar sama da fam miliyan 14 a watan Fabrairu.

Peace -- wanda ya shugabanci West Brom shekaru 13 -- yana da kashi 90 cikin 100 na hannun jarin kulob din.