Guinea ta nada Fernandez kociyanta

Luis Fernandez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guinea za ta kara da Swaziland a watan Yuni

Kasar Guinea ta dauki Luis Fernandez a matsayin sabon koci da zai horar da tawagar kwallon kafar kasar.

Hukumar kwallon kafar Guinea ce ta bayar da wannan sanarwar a inda ta ce kocin ya rattaba kwantiragin watanni 20 da kuma yarje-jeninar za a iya tsawaita zamansa.

An ba Fernandez, mai shekaru 55, ragamar ya kai kasar gasar cin kofin Afirka a shekarar 2017 da kuma kofin duniya a 2018.

Kocin wanda tsohon dan kwallon Faransa ne ya horar da tawagar kwallon kafar Israel da kuma kulob din Paris St Germain ta Faransa.

Guinea za ta fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2017 da Swaziland a cikin watan Yuni.