Madrid ta saka Odegaard a wasa da Almeria

Martin Odegaard Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Madrid tana mataki na biyu a kan teburin La Liga

Real Madrid ta saka Martin Odegaard a karon farko cikin 'yan wasan da za su fafata da Almeria a gasar La Liga da za su yi ranar Laraba.

Dan kwallon, mai buga wasan tsakiya, wanda manyan kungiyoyin Turai suka bukaci dauka a bara, ya koma Madrid ne a watan Janairun bana.

Odegaard, mai shekaru 16 wanda ya buga wa Norway wasanni hudu ya kuma yi wasanni tara da karamar kungiyar Madrid wato Castilla.

Haka kuma koci Carlo Ancelotti ya gayyato karin 'yan wasa biyu daga Castilla da suka hada da Borja Mayoral da kuma Diego Llorente.

Madrid tana fama da rashin manyan 'yan wasanta da suke yin jinya da suka hada da Gareth Bale da Luka Modric da kuma Karim Benzema.