An kara kudin lashe gasar Wimbledon da £120,000

Wimledon Prize
Image caption Za a fara gasar bana daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuli

An kara kudin da za a lashe a gasar kwallon tennis ta Wimbledon a inda zakarar bana zai karbi kudi da zai kai £1.88m.

Hakan na nufin an samu karin kudi da ya kai £120,000 ga duk dan wasan da ya lashe gasar bana.

Jumullar kudin da za a gudanar da gasar a filin wasa na All England zai karu zuwa £26.75m, fiye da bara da aka kashe £25m.

Haka kuma an kammala gyaran filin wasa na 14 da na 15 da hakan zai sa a samu Karin 'yan kallo zuwa 39,000 fiye da 38,800 a bara.

An kuma kara dasa na'urar da take tantance idan kwallo ta fita waje a filin wasa na 12 da kuma na 18 jumulla ana da guda shida kenan

Za a fara gasar cin kofin bana daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 12 ga watan Yuni.

Ga jerin kudaden da za a lashe a Wimbledon 2015

  • Total: £26.75m (+7%)
  • Singles: £1.88m (+7%)
  • Doubles: £341,250 (+5%)
  • Mixed doubles: £100,800 (+5%)
  • Wheelchair doubles: £15,360 (+28%)