Schneiderlin ya gama gasar wasannin bana

Morgan Schneiderlin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Southampton tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki 57

Dan kwallon Southampton mai buga wasan tsakiya ya kammala buga wasannin Premier bana, bayan da ya ji rauni a gwiwarsa.

Dan wasan, mai shekaru 25, ya ji rauni ne a karawar da suka tashi wasa 2-2 a gasar Premier da Tottenham ranar Asabar.

Dan wasan ya taka rawar gani a kulob din a bana, a inda ya buga wa Southampton wasanni 30 ya kuma ci kwallaye biyar.

Schnerderlin ba zai buga wasanni hudu da suka rage a gasar Premier ba, wanda Southampton za ta yi da Sunderland da Leicester City da Aston Villa da kuma Manchester City.

Southampton tana mataki na bakwai a gasar Premier, tana kuma neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi.