Ya kamata a girmama Chelsea - Terry

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Chelsea ce ta lashe gasar kofin Carling a bana

Kungiyar Chelsea ta cancanci "a bata girma" bayan da ya saura nasara guda kafin ta zama zakarun Premier, in ji John Terry.

Terry ne ya zura kwallo ta biyu a wasan da Chelsea ta doke Leicester City da ci uku da daya a filin wasa na King Power.

A cewarsa, kungiyar na bukatar a girmamata bayan da magoya bayan Arsenal suka ce wasansu ba ya "kayatarwa".

Tsohon kyaftin din Ingila mai shekaru 34 ya ce "Mune muka fi kowacce kungiyar haskakawa a kakar wasa ta bana."

Chelsea za ta iya lashe gasar Premier a ranar Lahadi idan har ta doke Crystal Palace a Stamford Bridge a ranar Lahadi.