Karon battar Mayweather da Pacquiao

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran za a samu dala miliyan 400 a dalilin damben

'Yan sa'oi suka rage a yi karon battar damben zamani mafi tsada a tarihi tsakanin Floyd Mayweather da Manny Pacquiao a Las Vegas ta Amurka.

Ana sa ran fara karawar ne da asubahin Lahadi 3 ga watan Mayu da karfe 4:30 na agogon Najeriya, a filin MGM Grand Arena na Las Vegas,a Amurka.

Sai dai wasu rahotanni na cewa ba a tsayar da ainahin lokacin fara damben ba.

Damben wanda ake wa lakabi da damben karni, shi ne mafi tsada a tarihin boksin.

Ana sa ran Mayweather, Ba'amurke mai shekara 38, wanda bai taba rashin nasara ba a dambensa 47, ya samu dala miliyan 200.

Shi kuwa abokin karawar tasa Manny Pacquaio dan Philipines, mai shekara 36, wand a dambensa 64 ya yi nasara a 57 da shan kashi a 5 zai samu dala miliyan 100.

Wanda kuma ya yi nasara zai dauki kambuna uku na ajin matsakaita nauyi na hukumomin WBC da WBA da kuma WBO.