Juventus ta lashe Serie A na hudu a jere

Juventus FC
Image caption Juventus ta dauki kofin Serie A na hudu a jere kuma na 31 jumulla

Kungiyar Juventus ta lashe kofin Serie A na Italiya karo na hudu a jere, bayan da ta doke Sampdoria da ci daya mai ban haushi ranar Asabar.

Tun kafin karawar Juve na bukatar maki daya ne ta dauki kofin bana sai gashi ta samu maki uku a karawar da ta yi a filin wasa na Luigi Ferraris.

Dan wasan Chile Vidal ne ya ci kwallo daya tilo da ka, bayan da ya samu tamaula daga bugun da Stephan Lichsteiner ya yi wo masa.

Jumulla Juventus ta dauki kofi na 31, kuma karon farko da koci Massimiliano Allegri ya jagoranci kungiyar.

Allegri, mai shekaru 47, ya fara horar da Juventus a farkon kakar wasan bana, bayan da Antonio Conte ya ajiye aikin kwana guda da 'yan wasa suka dawo daga hutu a bara.