West Brom ta doke Man United a Old Trafford

Man United West Brom
Image caption Karo na uku kenan da aka doke United a Premier a jere tun a shekarar 2001.

Manchester United ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun West Brom Albion gasar Premier wasan mako na 35 da suka yi a Old Trafford.

United ce ta mamaye karawar tun fara wasan, bayan da aka dawo wa daga hutu ne Chriss Brunt ya ci kwallo a bugun tazara a inda kwallo ta doki Jonas Olsson ta kuma shiga raga.

Wannan shi ne karon farko da Tony Pulis ya samu nasara a kan United, kuma West Brom ta hada maki 40 ta kuma koma matsayi na 13 a teburin Premier.

Haka kuma United ta yi rashin nasara a wasannin Premier uku a jere kenan, wacce Chelsea da Everton suka doke ta baya, wanda rabon da ta yi haka tun a shekarar 2001.

United din tana matakinta na hudu a teburin Premier da maki 65, za kuma ta ziyarci Crystal Palace a wasan mako na 36 ranar Asabar.