An yi kamfen din a kori Rodgers daga Liverpool

Rodgers Out Hakkin mallakar hoto twitter Rodgers out
Image caption Jirgin da ya yi shawagi a kan filin Liverpool dauke da sakon a kori Rodgers a dauko Rafa

Wani karamin jirgin sama ya yi shawagi a kan filin Anfield dauke da kyalle mai sakon "A sallami Rodgers a dauko Rafa" daf da za su kara da QPR a gasar Premier.

Wasu rukunan magoya bayan Liverpool ne da suke kiran kansu da sunan RodgersOutClub suka dauki nauyin kamfen din.

Liverpool ta nada Rodger a matsayin kocinta a watan Mayun 2012, kuma shi ne mai horar wa da ya yi shekaru uku bai dauki kofi ba tun bayan shekaru da dama.

Tsohon kocin Liverpool Rafa Benitez wanda ya jagoranci kulob din lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2005, ana sa ran zai bar Napoli a karshen kakar wasan bana.

Liverpool ta doke QPR da ci 2-1 tana kuma matakinta na biyar a teburin Premier da maki 61.