An fitar da Al Ahly daga Caf Champion League

Al Ahly Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Al Ahly ta dauki kofin zakarun Afirka sau takwas

Kulob din Moghreb Tetouan ya fitar da Al Ahly daga gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Afirka da ci 4-3 a bugun fenariti ranar Asabar.

A wasan farko da suka buga a Morocco, Moghreb Tetouan ne ya zura kwallo daya a raga, karawa ta biyu da suka yi a Masar Abdallah Said ne ya ci wa Al Ahly kwallo daya tilo.

Hakan ya sa suka buga fenariti a inda Moghreb Tetouan na Morocco ya fitar da Al Ahly wacce ta lashe kofin karo takwas daga gasar.

Karawar da suka yi a Masar din ranar Asabar an yi ne babu 'yan kallo saboda dalilin tsaro.