Al Ahly ta raba gari da koci Juan Carlos

Juan Carlos Garrido. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar Asabar aka fitar da Al Ahly daga gasar zakarun kungiyoyin Afirka

Zakarar kofin gasar Masar Al Ahly ta sallami kocinta Juan Carlos Garridos daga jan ragamar kulob din.

Al Ahly ta sanar da cewar ta yi hakan ne sakamakon fitar da ita da aka yi daga gasar cin kofin Zakarun Afirka da Moghreb Tetouan ta Morocco ta yi a ranar Asabar.

Kocin, mai shekaru 46, ya sanar ta intanet cewar daraktan kulob din ne ya sanar da shi baka da baka cewar ba zai ci gaba da horar da Al Ahly ba.

Juan Carlos ya kama aiki da Al Ahly ne a watan Yulin 2014, a inda ya jagoranci kulob din lashe Super Cup na Masar da kuma Confederation Cup na Afirka a kakar farko da ya fara aiki.

Kocin ya shiga matsi ne tun bayan da kulob din ya kasa taka rawar gani a gasar bana, a inda ya koma mataki na uku a kan teburi maki 11 tsakani da Zamalek wacce ke matsayi na daya.