Yarima Ali zai janye daga takarar kujerar Fifa

Prince Ali Bin Al-Hussein Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yarima Ali Bin Al-Hussein yana son a marawa dan takara daya domin ya fafata da Sepp Blatter

Dan takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Yarima Ali Bin Al-Hussein yana duba yiwu war janye wa daga takarar kujerar.

Yariman ya ce yin haka yana fatan zai sa a samu dan takara tilo da zai fafata da Sepp Blatter, kuma yana son a samu wanda ya dace ya jagoranci hukumar.

Yarima Ali na Jordan yana kalubalantar kujerar Sepp Blatter tare da Michael Braag na Netherland da kuma Louis Figo na Portugal.

Blatter, mai shekaru 78, yana neman a sake zabensa karo na biyar, inda mambobin hukumar su 209 za su gudanar da zaben ranar 29 ga watan Mayu.

Yarima Ali wanda zai bar kujerar kwamitin amintattu na Fifa ya ce yana fatan za a samu shugaban da zai kawo ci gaba a hukumar.