Arsenal ta dauki maki uku a kan Hull City

Ramsey Carzola Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Arsenal tana matsayi na uku a teburin Premier da maki 70

Kungiyar Arsenal ta doke Hull City da ci 3-1 a gasar Premier da suka yi ranar Litinin a KC Stadium.

Arsenal ta fara zura kwallo ta hannun Sanchez a minti na 28 da fara wasa, kuma Ramsey ya ci ta biyu, sannan Sanchez ya kara kwallonsa ta biyu kuma ta uku a wasan daf da za a tafi hutu.

Hull City wacce ta karbi bakuncin Arsenal din ta cire kwallo daya ta hannun Quinn bayan minti 11 da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Arsenal wacce ke da kwantan wasa daya ta hada maki 70, tana kuma mataki na uku a teburin Premier, a inda Hull City ke matsayi na 16 a teburin.

Ranar Litinin mai zuwa Arsenal za ta karbi bakuncin Swansea a Emirates, ita kuwa Hull City za ta karbi bakuncin Burnley ranar Asabar.