"Daukar Premier ladan dana dawo Chelsea ne"

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Chelsea ta dauki kofin Premier bana duk da saura wasanni uku a kammala gasar

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ce daukar kofin Premier da ya yi ladan hatsarin da ya dauka na koma wa horar da Chelsea karo na biyu ne.

Dan wasan da ya fi yin fice a gasar Premier Eden Hazard ne ya ci kwallon da suka doke Crystal Palace da ya ba su damar lashe kofin bana.

Mourinho ya ce zai ci gaba da horar da tamaula a Chelsea har tsawon lokacin da mamallakin kulob din ya bukace shi ya yi.

Kocin ya lashe kofin Premier ne a kakar wasan farko da ya dawo kulob din kuma karo na uku da ya yi jumulla a Chelsea.

Mourinho ya ce daukar kofin Premier da ya yi ladan hatsarin d ya dauka ne bisa dawo wa horar da kulob din, bayan nasarorin da ya samu a baya.