Benzema ba zai buga karawa da Juventus ba

Karim Benzema Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ta dauki kofin zakarun Turai sau 10, ta kuma kai wasan daf da karshe a gasar bana

Dan kwallon Faransa Karim Benzema ba zai buga wa Real Madrid gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Juventus ba a wasan daf da karshe.

Benzema, mai shekaru 27, ya ci kwallaye 22 a gasar bana, sai dai ba zai buga karawar da Madrid za ta yi da Juventus a Italiya ba, sakamakon rashin samun saukin raunin gwiwarsa.

Sai dai kuma Gareth Bale zai buga fafatawar, bayan da ya yi wasa ranar Asabar a lokacin da Madrid ta doke Sevilla a gasar La Liga wasan mako na 35.

Ita kuwa Juventus tana sa ran 'yan wasanta biyu Andrea Pirlo da kuma Giorgio Chiellini su kara a wasan.

'Yan wasan biyu sun zauna ne a benci a wasan da Juventus ta doke Sampdoria da ci 1-0, wanda ya sa ta dauki kofin Serie A na bana na hudu a jere na 31 jumulla.