An raba rukunin gasar kofin zakarun Afirka

Entente Setif Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Entente Setif mai rike da kofin zakarun Afirka na bara

A karon farko an hada kungiyoyin kwallon kafa uku daga Algeria a rukuni guda, a gasar cin kofin zakarun Afirka.

Mai rike da kofin, Entente Setif za ta kara da USM Alger da MC Eulma dukkansu daga Algeria sai kuma Al Merreik ta Sudan da suka cika su hudu a rukuni na biyu.

TP Mazembe ta Jamhuriyar Congo za ta fafata da Smouha ta Masar da Moghreb Tetouan ta Morocco da kuma Al Hilal ta Sudan a rukunin farko.

An raba rukunan ci gaba da wasannin kofin zakarun Afirka ne a hedikwatar hukumar kwallon kafar Afirka ne a Alkahira ranar Talata.

Za a fara wasannin ne a cikin watan Yuni, kuma kungiyoyi hudu ne za su kai wasan daf da karshe da shi kuma za a yi a watan Satumba da Oktoba, sannan a buga wasan karshe gida da waje a watan Oktoba da Nuwamba.

Ga yadda aka raba rukunin ci gaba da wasannin:

Rukunin A: Smouha (Masar), Moghreb Tetouan (Morocco), TP Mazembe Englebert (DR Congo), Al Hilal (Sudan)

Rukunin B: Entente Setif (Algeria, holders), USM Alger (Algeria), Al Merreikh (Sudan), MC Eulma (algeria)