Likitoci sun yi wa Sturridge aiki a kugunsa

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto Daniel Sturridge
Image caption Liverpool tana mataki na biyar a teburin Premier, saura wasanni uku a kammala gasar bana

Likitoci sun yi nasarar yi wa dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge aiki a kugunsa a Amurka.

Dan wasan, mai shekaru 25, dan kwallon Ingila ya buga wasanni biyu tun lokacin da ya ji raunin a karawar da suka yi da Manchester United ranar 22 ga watan Maris.

Sturridge ya ci kwallaye 24 daga wasanni 24 da ya yi a bara, amma a bana yana fama da yin jinya karo da dama inda ya buga wa Liverpool wasanni 18.

Wannan ne karo na biyu da dan kwallon ya ziyarci Amurka domin warware matsalar raunin da yake ji akai-akai.