Mourinho zai tsawaita kwantiraginsa a Chelsea

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zuwan kocin Chelsea ne ya daukar mata kofin Premier farko bayan shekaru 50 da ta lashe shi

Kociyan Chelsea Jose Mourinho na daf da tsawaita kwantiraginsa da Chelsea, bayan da ya lashe kofin Premier bana karo na uku kenan.

Mourinho, mai shekaru 52, wanda ya koma Chelsea karo na biyu kan yarjejeniyar shekaru hudu a watan Yunin 2013, zai rattaba kwantiragi mai tsawo da zai horar da kulob din.

A karon farko da ya fara kocin Chelsea tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007 ya dauki kofin Premier biyu da League Cup biyu da kuma kofin kalubale.

Daga nan ne kuma ya koma Inter Milan bayan da suka samu sabani tsakaninsa da mamallakin kulob din Roman Abramovich.

Bayan da ya dawo Chelsea a karo na biyu ya ce zai ci gaba da zama a kulob din iya tsawon lokacin da mai kulob din ya bukace shi ya yi.