Juventus ta zura wa Real Madrid kwallaye 2-1

Juventus FC Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Juventus ta dauki kofin Serie A na 31 jumulla a ranar Asabar

Juventus ta doke Real Madrid da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da karshe karon farko da suka yi a Italiya ranar Talata.

Alvaro Morata ne ya fara ci wa Juventus kwallo a minti na 8 da fara wasan, a inda Ronaldo ya farke wa Madrid kwallon, kafin Carlos Tévez ya kara ta biyu a ragar Madrid a bugun fenariti.

A ranar Asabar ce Juventus ta lashe kofin Seria A karo na hudu a jere kuma na 31 jumulla, bayan da ta doke Sampdoria da ci daya mai ban haushi.

Madrid ce ke rike da kofin bara kuma na 10 da ta dauka jumulla.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Juventus a wasa na biyu ranar laraba 13 ga watan Mayu a Santiago Bernabeu.