"Da wuya a hana Messi burgewa a wasa"

Lionel Messi
Image caption Lionel Messi ya ce Barca za ta dauki fansa a kan Bayern Munich

Kociyan Bayern Munich Pep Guardiola ya ce Lionel Messi ya kware wajen murza leda kuma abu ne mai wahala a hana shi haskakawa a wasa.

Bayern da Barca za su fafata a Nou Camp a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba a wasan farko na daf da karshe a gasar.

Guardiola ya ce "Babu wani mai horarwa da zai iya cewa ga yanda za a hana Messi taka leda, musamman da yake kan ganiyarsa watanni hudu zuwa biyar, ya kware matuka".

Kociyan ya horar da Barca shekaru hudu tamaula tun daga shekarar 2008, a inda ya dauki kofunan La Liga uku da na zakarun Turai biyu da na zakarun kungiyoyin kwallon kafa na duniya biyu.

Guardialo mai shekaru 44 ya kuma buga wa Barcelona tamaula tsawon shekaru 11 daga tsakanin 1990 zuwa 2001.