Munich na son Lewansdowski ya buga wasa da Barca

Robert Lewansdowski Hakkin mallakar hoto Bayern Munich
Image caption Dan kwallon ya ji rauni ne a gasar kofin Jamus da Borrussia Dortmund

Bayern Munich na son Robert Lewandowski ya buga karawar da za su yi da Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba.

Dan wasan zai taka leda ne sanye da abin rufe fuska saboda karya hanci da mukamuki da ya yi a lokacin da ya yi karo da golan Borussia Dortmund Mitchell Langerak a wasan daf da karshe na cin kofin Jamus.

Jeremy Mathieu shi ne dan kwallon Barcelona da ba zai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi.

Wasu daga cikin 'yan wasan Bayern ma suna fama da jinya, cikinsu har da Arjen Robben da Franck Ribery da David Alaba da kuma Holger Badstuber.

Shugaban Barcelona Josep Bartomeu ya ce 'yan wasansu ba za su shagala da fuskantar tsohon kocin kulob din Pep Guardiola ba.

Guardiola, mai shekaru 44, ya dauki kofuna 14 a Barcelona a shekaru hudu da ya yi, a inda ya koma Bayern Munich a shekarar 2013.