McClaren ya ki ya karbi horar da Newcastle

Steve McClaren Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Steve McClaren zai ci gaba da horar da Derby mai buga Championship

Steve McClaren ya ki amincewa da tayin da aka yi masa ya jagoranci Newcastle sauran wasanni uku a gasar Premier bana.

Newcastle ta tuntubi McClaren, mai shekaru 54, mai horar da Derby idan zai maye gurbin John Carver bayan da Leicester ta doke su 3-0 a gasar Premier ranar Asabar.

Tuni McClaren ya sanar da cewar ba zai bar horar da Derby ba wacce take buga gasar Championship a bana.

Newcastle ta amince da Carver, mai shekaru 50, ya ci gaba da horar da kungiyar zuwa karshen kakar wasan bana.

Kungiyar dai tana mataki na 15 a kan teburin Premier, wanda saura maki biyu ya rage mata ta shiga cikin jerin kungiyoyin da za su iya barin gasar Premier.