Adebayor ya yi korafi a shafin Facebook

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallon Adeboyr ta ja baya

Dan kwallon Tottenham Emmanuel Adebayor ya fito fili ya bayyana wasu matsalolin cikin gida da yake fuskanta da suka janyo masa tsaiko a kwallonsa.

A ranar talata Adebayor mai shekaru 31, ya wallafa wani dogon sako a shafin sada zumunta na Facebook inda yake bayar da haske a kan dalilin abinda ya bayyana a cikin watan Maris a matsayin wani halin ha'ula'i da ya shiga.

A rubutun Adebayor ya bayyana irin nauyin dake kansa na kula da iyalinsa ta fuskar kudi da kuma rikicin cikin gidansu.

Sai dai ya bukaci masu karanta rubutun nasa da su saka a zuciyar su cewa, ya bara ne a yanzu ba wai don ya fallasa danginsa ba ne.

Ya ce, yana so ne sauran iyalai na Afrika su yi koyi daga gare shi.

Adebayor yace ya rufe wannan labari tun tuni to amma ya ce, yana gani a yanzu ya dace sauran jama'a su san abinda ke faruwa.

Ya ce gaskiya ne ya kamata a warware matsalar gida a cikin gida ba a bainar jama'a ba, to amma yana yin haka ne da fatan dukkan iyalai za su iya yin koyi da abunda ya faru da shi.

Rayuwar iyalin Adebayo mai sarkakiya ta sa kulob din Tottenham ya ba shi hutu, inda aka jiyo dan wasan gaban a lokacin na cewa mahaifiyarsa na yi masa tsafi don ta cutar da shi.

Ga alama sakon nasa na bayyane, wani kokari ne na amsa wasu tambayoyi na abinda ya sa aka bar shi ya koma gida.

A wasanni 17 da yayi wa kulob din na London a kakar bana, Adebayo ya ci kwallo sau biyu kawai.