Al Ahly ta nada Mabrouk sabon kocinta

Al Ahly Egypt Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Asabar aka fitar da Al Ahly daga gasar cin kofin zakarun Afira na bana

Kungiyar Al Ahly ta masar ta dauki Fathi Mabrouk a matsayin sabon kociyanta domin maye gurbin Juan Carlos Garrido da ta sallama.

Zakarar kofin gasar Masar ta sallami Juan Carlos Garridos sakamakon fitar da ita da aka yi daga gasar cin kofin Zakarun Afirka da Moghreb Tetouan ta Morocco ta yi.

Mabrouk, wanda yake horar da karamar kungiyar Al Ahli ya taba jan ragamar babbar kungiyar, bayan da aka sallami Mohamed Youssef.

Sabon kocin zai jagoranci wasan da za ta yi da Rocky El-Nasr a gasar cin kofin gasar Masar ranar Laraba.

Al Ahly tana mataki na uku a teburin gasar Masar da maki 46 da tazarar maki 11 tsakaninta da Zamalek wacce ke mataki na daya a kan teburin.