An yi wa Benni McCarthy fashi a kanti

Benni McCarthy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption McCarthy ya lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2004

An yi wa tsohon dan kwallon Afirka ta Kudu Benni McCarthy fashi a shagon aski a birnin Johannesburg.

McCarthy, mai shekaru 37, ya hadu da 'yan fashin ne a shagon da barayin suka shiga a inda suka kwace masa abubuwa.

Eja dinsa Percy Adams ya ce daya daga 'yan fashi ya nuna masa bakin bindiga sannan ya umarce shi ya ba shi dan kunne da zoben bikinsa.

Adams din ya kuma ce 'yan fashin ba su raunata McCarthy ba, haka kuma ba su hari wadan da suke cikin shagon ba.

A bara aka kashe golan Afirka ta Kudu Senzo Meyiwa har lahira a Johannesburg. 'Yan sanda na yin bincike kan lamarin.