"Zargin da ake yi wa Bale ba shi da tushe"

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale ya yi fama da jinyar rauni da bai buga wasa da Atletico ba

Eja din Gareth Bale ya yi watsi da zargin da aka yi cewar dan wasan bai taka rawar gani ba a karawar da Juventus ta doke Madrid da ci 2-1 ranar Lahadi.

Alvaro Morata ne ya fara ci wa Juventus kwallo a minti na 8 da fara wasan, a inda Ronaldo ya farke wa Madrid kwallon, kafin Carlos Tévez ya kara ta biyu a ragar Madrid a bugun fenariti.

Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane ne ya ce Madrid ta buga gasar ne da 'yan wasa 10 a cikin fili, inda ya ce Bale bai yi kuzari ba a karawar.

Jonathan Barnett ya ce bai kamata a dinga la'akari da fadar albarkacin bakin wasu mutane da ba su san me suke yi ba, sannan suka kasa samun ci gaba a fagen shugabanci ba.

Bale, mai shekaru 25, wanda ya koma Madrid a shekarar 2013, shi ne wanda ya yi karancin taka tamaula da bai wa abokin wasa a Madrid da aka doke su 2-1 a Turin.