An shigar da Manny Pacquiao gaban kuliya

Manny Pacquiao Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayweather ya ce isai mutum ya yi rashin nasara a wasa ke yin korafi

An shigar da dan dambe Manny Pacquiao a kotu, wanda Floyd Mayweather ya doke a Las Vegas a makon da ya wuce.

An kai dan wasan kara ne bayan da ya yi korafin cewar ciwon da yake jinya a kafada ne ya rage masa karsashi a damben da ya yi ranar Asabar.

Cibiyar wasannin motsa jiki ta Navada ce ta kai dan damben kara, a inda ta ce bai sanar da raunin da yake dauke da shi ba a lokacin taron amsa tambayoyi kafin karawar.

Idan aka samu dan damben da laifi za a iya yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekara daya zuwa hudu da cin tarar da za ta kai $5,000.

Pacquiao ya zagi rashin nasarar da ya yi a hannun Mayweather kan raunin kafadarsa, a inda ya ce ciwon ya hana shi amfani da hannun kamar yadda ya kamata.