Za a dakatar da wasannin kwallon kafar Spaniya

Madrid vs Barca
Image caption Hukumar ta ce za ta dakatar da dukkan wasannin kasar ranar 16 ga watan Mayu

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta ce za ta dakatar da wasannin kasar, bisa takaddama da take yi da gwamnati kan hakkin nuna gasar a talabijin.

Hukumar ta ce za ta tsaida dukkan wasannin kasar daga ranar 16 ga wayan Mayu.

A sanarwar da hutumar ta fitar ta ce ba ta ji dadi ba da kaso 4.5 cikin dari kawai ta karba daga gwamnati, duk da dai suna ci gaba da tattaunawa kan batun.

A gasar La Liga kasar Barcelona ce ke kan gaba a teburin gasar, a inda ta bai wa Real Madrid tazarar maki biyu duk da saura wasanni uku a kammala gasar bana.