Dan Nigeria Ujah ya zai koma Werder Bremen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ujah na murnar zura kwallo

Dan kwallon Nigeria, Anthony Ujah zai bar kungiyar Cologne daga Werder Bremen a Jamus.

Dan shekaru 24, ya zura kwallaye 10 a kakar wasa ta bana, inda ya taimakawa Cologne ta haye siradin ci gaba da murza leda a gasar Bundesliga.

Daga farko Ujah ya soma take leda ne a Mainz 05 kafin ya koma Cologne.

Gudunsa da kuma gogewarsa ta sa yana da farin jini a tsakanin magoya bayan kulob din.

Ujah ya zura kwallaye 24 a cikin wasanni 62 da ya buga wa FC Cologne.